1

1 Annabcin Obadiya ke nan. Wannan shi ne abin da Ubangiji Allah ya ce a kan al'ummar Edom. Ubangiji ya aiki manzonsa wurin sauran al'umma, Mun kuwa ji saƙonsa cewa, “Ku zo! Mu tafi mu yi yaƙi da Edom!”

2 Ubangiji ya ce wa al'ummar Edom, “Zan maishe ki ƙanƙanuwa a cikin sauran al'umma, Za a raina ki ƙwarai.

3 Girmankanki ya yaudare ki, Kina zaune a kagara, a kan dutse, Wurin zamanki yana can ƙwanƙolin duwatsu. Don haka a zuciya kike cewa, ‘Wa zai saukar da ni ƙasa?’

4 Ko da yake kina shawagi can sama kamar gaggafa, Gidanki kuma yana can cikin taurari, Daga can zan saukar da ke,” in ji Ubangiji

5 “Idan ɓarayi sun shiga gidanki, Idan kuma 'yan fashi sun shiga gidanki da dare, Yaya za su washe ki? Za su sace abin da ya ishe su ne kaɗai, Idan kuma ɓarayin 'ya'yan inabi sun shiga gonar inabinki, Za su bar miki kala kurum.

6 Isuwa, wato Edom, ga taskarka, An washe ta ƙaƙaf!

7 Waɗanda kake amana da su, Za su kore ka daga ƙasarka. Mutanen da suke amana da kai, Za su yaudare ka, Su ci ka da yaƙi. Abokan nan naka da kake ci tare da su za su kafa maka tarko, Sa'an nan su ce, ‘Ina dukan wayon nan nasa?’ ”

8 Ni Ubangiji na ce, “A ranar da zan hukunta Edom, Zan hallaka masu hikimarka, Zan shafe hikima daga dutsen Isuwa.

9 Jarumawanka za su firgita, ya Teman, Za a kashe kowane mutum daga dutsen Isuwa.

10 “Saboda kama-karyar da ka yi wa Yakubu ɗan'uwanka, Za a sa ka ka sha kunya, Za a hallaka ka har abada.

11 A ranan nan ka tsaya kawai, A ranar da abokan gāba suka fasa ƙofofinsa. Suka kwashe dukiyarsa, Suka jefa kuri'a a kan Urushalima. Ka zama kamar ɗaya daga cikinsu.

12 Ba daidai ba ne ka yi murna Saboda wahalar da ta sami ɗan'uwanka. Ba daidai ba ne ka yi farin ciki Saboda halakar mutanen Yahuza. Ba daidai ba ne ka yi musu dariya A ranar wahalarsu.

13 Ba daidai ba ne ka shiga ƙofar jama'ata A ranar da suke shan masifa. Ba daidai ba ne ka yi murna A kan bala'in ɗan'uwanka. Ba daidai ba ne ka washe dukiyarsa A ranar masifarsa.

14 Ba daidai ba ne ka tsaya a mararraba, Don ka kashe waɗanda suke ƙoƙarin tserewa. Ba daidai ba ne ka ba da waɗanda suka tsere a hannun maƙiyansu A ranar wahala.”

15 “Ranar da ni Ubangiji zan shara'anta al'ummai duka ta zo kusa, Ke, Edom, abin da kika yi, Shi ne za a yi miki. Ayyukanki za su koma a kanki.

16 Kamar yadda kuka sha hukunci a kan tsattsarkan dutsena, Haka dukan sauran al'umma za su yi ta sha. Za su sha, su yi tangaɗi, Su zama kamar ba su taɓa kasancewa ba.”

17 “Amma za a sami waɗanda za su tsira daga Dutsen Sihiyona, Dutsen zai zama wuri ne mai tsarki. Jama'ar Yakubu za ta mallaki mallakarta.

18 Jama'ar Yakubu za ta zama kamar wuta, Jama'ar Yusufu kuwa kamar harshen wuta, Jama'ar Isuwa za ta zama kamar tattaka. Za su ƙone ta, su ci ta, ba wanda zai tsira. Ni Ubangiji na faɗa.”

19 Isra'ilawan da yake Negeb za su mallaki dutsen Isuwa, Waɗanda suke a filaye na Yahuza za su mallaki ƙasar Filistiya. Isra'ilawa za su mallaki yankin ƙasar Ifraimu da Samariya, Jama'ar Biliyaminu za su mallaki Gileyad.

20 Rundunar masu zaman talala na Isra'ilawa Za su mallaki Kan'aniyawa har zuwa Zarefat. Masu zaman talala na Urushalima da suke a Sefarad Za su mallaki biranen Negeb.

21 Isra'ilawa za su hau Dutsen Sihiyona, su cece shi, Za su mallaki dutsen Isuwa, Ubangiji ne Sarki.